Mutanen da aka kama an samesu da makamai da albarusai masu yawa hade da wasu motoci da tsabar kudi.
Rundunar 'yansandan ta gano baburan hawa guda biyu da shanu dari da saba'in da daya da kananan dabbobi dangin tumaki da awaki guda dari da talatin da ukku.
Kwamishanan 'yansandan Alhaji Haliru Gwandu yace sun ceto mutane hamsin wadanda aka sace ana garkuwa dasu domin neman kudin fansa. Wadanda 'yansandan suka kama sun haura arba'in kuma dukansu suna da suffar Fulani. Cikin wadannan, fiye da ishirin da biyar suna gidan yari, kana ishirin da ukku suna kulle a ofishin 'yansanda.
Alhaji Gwandu yace mutanen basu da wani aiki illa su kama mutane su tambayesu kudi kafin su sallamesu.
Dangane da dazuzukan dake kewayen Bauchi kwamishanan yace sun baza 'yansanda cikinsu kuma suna sintiri dare da rana.
Cikin masu satar shanu da karguwa da mutane da aka kama wasu sun zanta da Muryar Amurka. Wani Suleiman daga Ningi yace shanu 31 suka sato har aka kamashi.Wani kuma cewa yayi sun sace wani mutum ne domin abokinsa yace yana jin haushinsa, suka dora masa kudin da zai biya kafin su sakeshi. Sun dorawa mutumin nera dubu dari biyar suka tafi da dansa.
Yayinda ake hada wannan rahoto wasu masu satar mutane sun kewaye garin Nabardo inda suka tilastawa mutanen garin ficewa daga gidajensu.
Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.