A jihar Neja an gudanar da wasu addu'o'in musamman domin ganin an sako ragowar 'yan matan Chibok da na garin Dapchi dake jihar Yobe da aka sace makon jiya.
Akasarin mahalarta taron addu'o'in na cikin wani yanayin bacin rai saboda rashin sanin makomar yaran da aka sace kwana kwanan nan da yawansu ya kai 110. Malam Yahaya Mahmud daya daga cikin 'yan kungiyoyin fararen hula da suka shirya addu'o'in ya ce babu abun da zasu iya yi illa su roki Allah Ya sa a kubutosu tare da sauran 'yan matan Chibok lafiya.
A cewar Malam Mahmud rashin kulawa ne ya sa aka kara samun sace yara kamar yadda 'yan ta'addan suka yi a Chibok kusan shekaru hudu ke nan. Ya ce sakacin daga wajen gwamnati ne. Ijishi duk makarantun dake yankin arewa maso gabas yakamata a girke masu jami'an tsaro.
Wasu daga cikin mahalarta taron, su ma sun yi nasu furucin. Muhammad Saidu Etsu cewa ya yi shekaru hudun da suka gabata an sace 'yan mata sai kuma gashi an sake sace wasu, wannan abu ne da hankali ba zai dauka ba musamman gabanin karatowar siyasa. Ya ce basu san manufar jama'a ba dalili ke nan suka zo su yi addu'a.
Aisha Wakaso wata dake zaune a Minna ta ce ranta ba karamin baci ya yi ba akan lamarin. Lokacin da na farko ya faru an ce siyasa ce amma kuma sai gashi ya sake faruwa to ko menene dalilin hakan yanzu ita bata sani ba, injita.
Ta roki 'yan ta'addan da su yi hakuri. Yaran da suke sacewa ba su ne suka yi masu laifi ba in ma akwai laifin.
Adduo'in da aka gudanar sun kunshi na Musulunci da Kiristanci.
A saurari rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.
Facebook Forum