Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Sudan Ta Kudu Ta Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Raba Iko


 Shugaba Salva Kiir da shugaban 'yan tawaye Riek Machar
Shugaba Salva Kiir da shugaban 'yan tawaye Riek Machar

Gwamnatin Sudan ta Kudu ta sa hannun wata yarjejeniyar share fage tsakanin ta da wata babbar kungiyar ‘yan tawayen kasar domin raba iko, da zummar kawo karshen yakin basasar kasar  na kusan shekaru biyar.

Sai dai kuma wata gamayyar jam'iyyun hamayya 9 sun ki su sa hannu a wannan yarjejeniyar suna cewa sun dauki matakin saboda ba'a karbi shawarwari d a suka bayar ba.

Yarjejeniyar da Muryar Amurka ta samu damar gani, ta nuna cewa har yanzu shugaba Salva Kir zai ci gaba da zama shugaban kasar, yayin da shugaban ‘yan tawaye Riek Machar, zai ci gaba da rike tsohon mukaminsa na mataimakin shugaban kasa na farko.

Haka kuma yarjejeniyar ta bukaci a samar da majalisar dokoki mai mutane 550 a shirin mika mulki, sannan a samar da wasu mataimakan shugaban kasa mutane 4 kuma daya daga cikin su za ta kasance mace.

Kungiyar ta yankin kasashen Afirka ta Gabas ne da ake kira IGAD ta kasance mai shiga tsakani akan wannan yarjejeniyar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG