Da gagarumin rinjaye Majalisar Dokokin kasa ta yi na’am da bukatar da bangaren zartaswa ya gabatar da nufin samun izinin bai wa kasashe aminai damar girke sojojinsu, ganin yadda yaki da ta’addanci ke kara zafi a yankin Sahel matsalar da gwamnatin ta ce na iya yaduwa a illahirin kasashenn yammacin Afurka muddin ba a tsaurara matakai ba .
Kakakin majalisar dokokin kasa Seini Oumarou ya ce ‘yan majalissa 131 ne suka yi na’am da kudirin gwamnatin yayin da wakilai 31 suka yi watsi da shi.
An dai shafe tsawon jiya juma’a ana tafka mahawara a tsakanin bangarorin majalissar inda kowanne ke kokarin kare matsayinsa.
To sai dai ‘yan adawa sun yi ta kokarin ganar da gwamnatin ta Nijer abubuwan da ka iya biyo bayan wannan yunkuri na bai wa kasashen waje damar kafa sansani musamman kasar Faransa wace ta yi kaurin suna kamar yadda dan majalissa na RDR Canji Honorable Laouali Ibrahim Mai Jirgi ya bayyana.
Framinista Ouhoumoudou Mahamadou wanda ya hallara zauren majalisar don kare gyarar fuskar da ya yi wa manufofin gwamnatinsa a sashen da ke bayan ikan sha’anin tsaron kasa ya yi godiya a sakamakon hadin kan da gwamnatinsa ta samu daga majalisar dokoki . Ya na mai bada tabbacin za a sanar da ‘yan kasa matsayar da za a cimma a yarjejeniyoyin da za su rattabawa hannu a nan gaba da kasashen aminnai inda komai zai gudana da yawun sojojin Nijer ta yadda kasar za ta amfana sosai a sabuwar tafiyar da aka sa gaba.
A watan Fabrairun da ya gabata ne shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron a karshen wani taro da ya tattara shugabanin kasashen afurka ta yamma ya sanar da shirin kwashe rundunar sojan barkhane don mayar da ita Nijer sanadiyar tsamin dangantakar da ke tsakaninsa da gwamnatin mulkin sojan Mali to amma la’akari da yadda batun girke sojan waje ke haifar da tada jijiyoyin wuya a wajen wasu ‘yan kasa ya sa shugaba Mohamed Bazoum bullowa abin ta hanyar da kundin tsarin mulki ya yi tanadi, mafarin tuntubar Malajisar Dokokin kasa.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: