Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Ce Za Ta Gudanar Da Zaben Gaskiya


Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Gwamnatin Najeriya ta gargadi kasashen ketare akan yin katsalandan a harkokin ta. Kasar da ke yankin Afrika ta Yamma ta jaddada cewa za ta gudanar da zaben shugaban kasa na gaskiya da adalci a ranar 16 ga wata Faburairu dake tafe.

Da yake maida martani a kan sukar da Amurka da Birtaniya da kuma kungiyar Tarayyar Turai suka yi a kan dakatar da babban akalin Najeriya da shugaba Buhari ya yi ranar Jumma'a, mai Magana da yawun shugaban ya kare wannan matakin.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kudiri aniyar tabbatar da zaben gaskiya da adalci. wannan gwamnatin ba zata saba saba doka ba kuma ba zata amince a tsoma mata baki a cikin harkokinta ba, a cewar Mallam Garba Shehu a wata sanarwa da ya fidda ranar asabar da maraice.

An zabi shugaba Buhari mai shekaru 76 tsohon shugaban soja a shekarar 2015, yanzu yana kuma neman a sake zabensa karo na biyu a kasar da tafi kowace kasa a nahiyar Afrika yawan al’umma. Bangaren shari’ar kasar ne zai zartar da hukunci a kan duk wanda ya kalubalance sakamakon zaben shugaban kasa da na 'yan Majalissa, har zuwa matakin kotun koli.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG