Yayin da ake ta cece-kuce a jihar Taraba, tsohuwar Ministar Harkokin Mata Aisha Jummai Alhassan, ta musanta rahotannin da su ke cewa ta janye takararta ta gwamnar jihar.
Wannan ya na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan takara su ke ci gaba da gangamin yakin neman zabe da ke kara matsowa a Najeriya.
A zaben 2015, an fafata da Sanata Aisha Jummai Alhassan, wacce ake wa lakabi da Mamar Taraba, lokacin da wata kotu ta yanke hukunci cewa ita ce ta samu nasara, wanda daga baya ya zama ta leko ta koma.
Aisha ta ce, ta na nan a takararta, kuma za ta ci gaba da wannan fafutuka har sai ta ga abin da ya ture wa buzu nadi.
Wannan lamari ya na zuwa ne yayin da tawagar dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar APC, Sani Abubakar Danladi, ta sake fita gangamin yakin neman zabe, bayan wani hari da aka kai wa tawagar a Wukari.
Ga wakilinmu Ibrahim Abdul-Aziz da cikakken rahoton:
Facebook Forum