Gwamnatin Najeriya ta gargadi kasashen waje da kar su yi katsalandan a zaben kasar, ta na mai jaddada cewa kasar ta Yammacin Afurka za ta gudanar da zaben Shugaban kasa cikin adalci a ranar 16 ga watan gobe.
Da ya ke maida martani kan sukar da Amurka da Burtaniya da kuma Tarayyar Turai su ka yi, saboda dakatar da alkalin-alkalan Najeriya da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi, mai magana da yawun Shugaba Buhari ya kare wannan shawarar da Shugaban ya yanke.
"Gwamnatin tarayyar Najeriya ta himmantu ga gudanar da zabe cikin adalci da gaskiya. Wannan gwamnatin ba za ta karkatar da doka ba haka kuma ba za ta lamunta da duk wani shishshigi cikin harkokinmu ba,” a cewar mai magana da yawun Shugaban kasar Garba Shehu, a wata rubutacciyar takarda da daren Asabar, a cewar kafar labarai ta Reuters.
A wani karin bayani da ya yi jiya Lahadi, Shehu ya bayyana kasashen uku da abokan Najeriya, to amma sai ya ce ga dukkan alamu sukar da su ka yi “ta biyo bayan zato mara tushe, da kuma raina salon wannan dimokaradiyyar Afurkar.” Ya kara da cewa, “Babu daya daga cikin kasashenku da za ta bar alkalin da ke dabaibaye da rigingimu ya yi alkalanci, idan ba a warware matsalar ba.”
Facebook Forum