Gwamnatin jihar Legas ta bada umurnin rufe gidajen dake yankin Ikorodu bayan an gano ana anfani da gidajen wajen hako man fetur.
A sanarwar da gwamnatin ta bayar ta hannun kwamishanan yada labarai Mr. Steve Ayorinde ta bayyana cewa daukan matakin ya zama wajibi domin tabbatar da tsaro da kuma ceto rayukan al'umma dake cikin hatsari.
Gwamnatin jihar ta Legas tace ba zata saka ido ta ga ana yiwa tattalin arzikin kasar zagon kasa ba.
Kazalika gwamnatin ta sake bada sanarwar rufe wani otel da ta zarga da zama makafa wa masu garkuwa da mutane da kuma aikata miyagun laifuka. Tuni jami'an tsaro suka kewaye yankin da gidajen.
Gwamnati ta umurci mutanen dake zaune a yankin da su kauracewa unguwar domin gudun fadawa tarkon jami'an tsaro..
Alhaji Abdulmajjed Ali mataimakin sifeton 'yansandan Najeriya mai kula da jihohin Ogun da Legas ya tabbatar da daukan wannan matakin ta wayar tarho.
Wani Malam Abdul Kebbi yace tabbas akwai wasu da ak fitar dasu daga gidajensu domin gwamnati ta gano suna fasa bututun mai daga cikin gidajensu. Wasunsu sun fada hannun gwamnati wasu kuma sun gudu.
Ga rahoton Babangida Jibril da karin bayani.