Kwamishinan yada labaran jihar Ahmed Sajo, yace an kafa kwamitin ne don bincikar al’amarin, kuma duk rahotan da kwamitin binciken fitar tabbas za a yi amfani da shi wajen kawo karshen rigimar, da kuma kare faruwar makancin wannan tashin hankali da ka iya bullowa nan gaba.
A makon jiya ma an samu wani tashin hankali a yankin Kidimu dake karamar hukumar Demsa, inda rayuka fiye da goma suka salwanta bayan da wanda ya faru a karamar hukumar Girei duk dai a jihar Adamawa.
Kawo yanzu dai masana na ganin dole ne sai gwamnatoci a Najeriya sun tashi tsaye wajen magance wannan matsala da ake samu tsakanin Fulani Makiyaya da kuma Manoma, wadanda ke zama tamkar ‘dan Juma ne da ‘dan Jummai.
Saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz daga Yola.