Hukumar dake kula da basukan kasar ta gabatarda adadin bashin dake kan kasar. Hukumar tace bashin da ake bin Najeriya ya haura dalar Amurka miliyan dubu dari dara da rabi.
Bayanin ya fito ne a daidai lokacin da shugaban kasa Muhammad Buhari yake kokawa akan dimbin bashin da aka barwa Najeriya da kuma asusun gwamnati da ya taras warwas har ma yana cewa dole ne a dauki mataki na dawowa da kudaden da aka wawure.
Malam Sha'aibu Idris wani masanin tattalin arziki ya yi tsokaci akan dimbin bashin dake kan Najeriya. Yace na farko an riga an bar shiri tun rani. Yace Najeriya ta ci bashi daga kasar China domin ta gyara layin dogo. Amma da aka kawo bashin ba'a yi aikin ba.
Yace ba kuskure ba ne a ciwo bashi domin a gyara hanyar jirgin kasa saboda mutane zasu hau jirgin kuma daga kudaden da ake samu za'a biya bashin. Akan tashoshin jiragen sama ma an karbi basussuka amma har yanzu ba'a gama tashoshin ba. Wadanda aka gama basu da inganci kamar ta Yola da ruwan sama ya kwashe. Akan wutar lantarki an ciwo basussuka da dama amma babu wutar.
Misali an ciwo bashi daga bankin musulunci na Jiddah da sunan samar ma Jihar Kaduna ruwan sha amma bayan shekaru biyar da cin bashin babu abun da ak gani a kasa.
Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.