Shugaba kasa Muhammad Buhari ya bukaci gwamnoni su tabbatar cewa sun dauk duk wani mataki da ya kamata domin biyan albashin ma'aikatansu nan take ba tare da bata wani lokaci ba.
Ya kira gwamnonin su tabbatar sun rike amana da kwatanta gaskiya a wurin mulki domin tabbatar da an yaki cin hanci da karbar rashawa wadanda yanzu suka yiwa kasar Najeriya katutu.
Shugaban kasa ya yi alwashin farfado da tattalin arzikin kasa da kuma tabbatar da cewa ya toshe duk wata hanya ko kafar da ake wawure dukiyoyin jama'a ko kuma yin almubazaranci tare da baiwa gwamnonin karfin gwiwar cewa kowannensu ya kamata ya duba hanyoyin da zai samu kudin shiga a cikin jihohinsu ba tare da ciga da dogara akan asusun gwamnatin tarayya dari bisa dari ba.
Gwamnan Zamfara Yari yayi karin haske akan taron.
Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.