Babban Jamiyyar adawa a Najeriya PDP ta kara caccakar gwamnatin Muhammadu Buhari da nuna tana neman fakewa da cewar gwamnatin Jonathan ce ta rikita lamurra da ya sanya rashin shiga aikin gwamnatin ka’in da na’in .
Tun farkon mako dai PDP dai tace Buhari na bukatar adduar yan Najeriya domin tamkar ya karbi ragamar kasa ce ya rasa inda zai fara aiki kuma wata daya kenan PDP tace sabuwar gwamnatin bata cimma kome ba sai romon baka.
Sakataren yada labarai na jamiyyar PDP Olise Metuh cewa yayi.
‘’Sai shara karya suke yi suna kokarin jefa demokaradiyyar mu cikin halin oni ‘yasu.’’
‘’Gaskiya sun fara saka da mummunar zare’’
PDP dai ta baiwa shugaba Buhari kwanaki 10 ya nada majilisarsa ta zartaswa ku su dauka matukin motar ya kubbucewa wa APC.
Take dai fadar Gwamnatin shugaba kasa ta nuna tana aikin share tuannatin da PDP tayi wa gwamnati ne, inda wata majiya ma tace gwamnatin Buharin ta gano gwamnatin data shude ta bar bashir naira tiriliyan 7 a baitulmalin da idan anyi lissafi ba ko karfen fada.
Mai Mala Boni shine sakataren APC.
‘’Duk abinda dan jamiyyar PDP zaice a yanzu dole mu dauka magagin faduwa ce sabo da magagin ce bata sake su ba har yanzu, na biyu zaka ce suna so su dauke hankalin yan Najeriya daga ainihin bannar da suka yi domin su sace kudin kasar sun bar kasar a talauce sun rugurguza kame ba ci gaba kasa ta tsaya cik ita Magana idan maiyin ta wawa ne ai mai jinta ba wawa bane, kasar nan kam haka suka same ta ne? da suka yi shekaru 16 ai ba haka suka samu kasar nan ba sun samu kasar nan da kimanta da tattalin arzikin ta da karfin ta su suka ruguza kasar komai da ka sani sai da ya tabarbare a kasar nan, to wane ma bakin Magana suke dashi da zasu iya suce zasu yi wata Magana ta adawa wadda wani zai saurare su wani talakka a Najeriya zai saurare su, sai dai kasan duk a lokacin da azzalumi zaiyi Magana azzalumai yan uwan sa zasu saurare shi’.
Shi tsarin mulkin Najeriya ya bada lokacin da sabuwar gwamnati zata yan majilisar zartarwa ne ko a’a, Barister Zabairu Namama lauya ne mai zaman kansa a Abuja.
‘’Dokar kasa ta Najeriya ta baiwa shugaban kasa dama ya nada ministoci akan lokaci amma ba a bada waadin lokaci ba.’’
Wato Kana nufin tsarin mulki baice wata daya dole ne aga an nada ministoci ba, babu wani takamaiman waadi Kenan?
‘’Sani na dai da tsarin mulkin Najeriya matsayi na dai mutum lauya mai zaman kansa da yan shekaru da nayi a wannan aiki ban tsammani akwai inda dokar kasa ta bada waadi ba sai dai doka ta dora wa shugaban kasa nauyin ya tabbatar da cewa ya nada ministoci akan lokaci wadanda zasu taya shi gudanar da aikin shi na yau da kullun.’’
PDP ta bukaci ya bukaci shugaba Buhari ya damke yan cin hanci da rashawa amma tuni tayi kanda garkin kar binciken ya zama bita da kulli gay an PDP.
Da alamu dai shugaba Buhari ya samu hadin kan turai wajen dawo da kudaden da barayin biro suka wawure da adanawa bankunan ketare.
Ga Nasir Adamu El-Hikaya da cikakken rahoton