Sanarwar dake kunshe da bayanin ta fito ne daga ofishin shugaban ma'aikata na Najeriya wadda kakakin ofishin Alhaji Haruna Imrana ya rabtaba hannu a kai.
A sanarwar shugaban ya godewa daraktocin bisa ga aikin da suka yiwa kasa a kamfanin da yi masu fatan alheri bisa ga abun da zasu yi nan gaba.
Ana ganin babu shakka matakin yana cikin garambawul da shugaban yake son ya yiwa kamfanin wanda aka ce ya zama gadon bayan cin hanci da karbar rashawa a tarayyar kasar.
Wani tsohon minista a ma'aikatar man din Alhaji Umaru Dembo ya bayyanawa Muryar Amurka cewa matakin da shugaban kasa ya dauka yana da mahimmancin gaske a yakin da shugaban yace zai yi da cin hanci da rashawa, babakere da almundahana da kuma tabbar da an bi kaidodin aiki wurin gudanar da mulki a Najeriya.
Alhaji Dembo yace matakin yayi kyau da gaske domin zai hana cigaba da yin barna da suka saba yi. Yace za'a bincika irin wala wala da ake yi da cuwa cuwa da yawan yadda kudade ke bata. An dade ana koke-koke akan tabargaza da sama da fadi da ake yi da dukiyar kasa a kamfanin. Shin wai korar daraktocin kadai za'a yi yanzu? Yace babu wanda shugaban kasa zai bari. Dukansu sai an bincikesu.
Ga rahoton Umar Faruk Musa.