Kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa tun farko domin tsara matakan da yakamata a dauka akan cutar ya gabatar da rahotonsa ga gwamnati.
Majalisar ta yiwa rahoton gyaran fuska yadda za'a yi aiki dashi a tabbatar cutar bata yadu ba. Ministan yada labaran Najeriya Mr. Labaran Maku ya yi karin haske.
Duk wadanda suka yi muamala da Mr. Sawyer wanda ya shigo da cutar daga kasar Liberia yanzu gwamnati ta gano su ta kuma kebesu ana kuma dubasu har ma wasu sun fara rasa rayukansu. Ministan yace ciwo ne wanda ba zaka san kana dashi ba sai bayan sati uku. Cikin wadanda suka yi muamala da Mr. Sawyer shida sun kamu da cutar.
Akan maganin da aka fara gwadawa ministan yace sun ji akwai wani magani da aka yi anfani dashi a Amurka kuma wadanda aka ba sun fara samun sauki. Sabili da haka Najeriya ta rubutawa Amurka tana neman maganin. Ban da maganin gwamnati ta ji labari mai cewa namujin goro na warkar da cutar amma su basu tabatar da hakan ba.
Yanzu dai gwamnatin tarayya ta fara daukan matakan yekuwa a kafofin yada labarai daban daban domin fadakar da jama'a kan mahimmancin tsafta da yin anfani da abubuwan da suka kamata domin kada ciwon ya yadu.
Ga rahoton Umar Faruk Musa.