A taron manema labarai da kwamishinan kiwon lafiyan Jihar Legas yayi, Dr. Jide Idris yace babu gaskiya game da batun mutuwar likita.
Amma Dr. Idris ya bayanna cewa likitan na kebabben wuri da ake mata magani, kuma tana tare da sauran ma’aikatan kiwon lafiyan da suka kamu da cutar.
Dr. Nasir Sani Gwarzo, shine shugaban yaki da cutar a Najeriya “likitan bata rasu ba, tana nan ana yi mata jinya, amma mai kula da marasa lafiya daya ta rasu”.
Wannan cuta dai ta bullo ne a kasar Guinea, inda a halin yanzu ta dauki rayukan mutane sun kusa 1,000 a duk fadin yammacin Afirka.