Gwamnatin Najeriya, ta dauki kwararan matakai akan mummunar cutar nan ta Ebola, ganin yanda cutar ta kashe mutane masu dinbin yawa a Afirka.
Shugaban yaki da wannan cutar Dr. Nasiru Sani Kwarzo, yace sunanan suna ci gaba ta daukan matakan ganin cewa cutar bata ci gaba da shigowa Najeriya, ba.
Yace daga tashoshin jiragen sama da na ruwa da sauran bakin iyakokin Najeriya, da ake iya shigowa yanzu haka an dauki matakin da ya dace .
Dr. Gwarzo ya kara da cewa yanzu haka an kai naurori na wucin gadi zuwa manyan tashoshi wanda idan mutun na daga nesa za’a iya auna zafin jikinsa ba tare da ka tabashi ba.
Yace kuma za’a fadada inda basu kai ba za’a tabbatar cewa naurorin sun kai.
Ya kuma kara da cewa duk da rajin aikin da likitici keyi wasu sun kawo kansu domin taimakawa saboda wannan cutar.