Tace cutar bata yaduba domin ko a jihar Legas wadanda suka kamu da cutar suna wani kebabben wuri ne a asibitin dake Yaba.
Shugaban yaki da cutar ebola Dr. Nasir Sani Gwarzo ya zanta da Muryar Amurka. Yace cikin mutane bakwai da suka kamu da cutar biyu ne suka rasu. Duk inda aka samu labarin cutar ta bullo an tura jami'an kiwon lafiya amma ba daya da ya zame gaskiya a ciki. To sai dai ya ja kunne mutane su guji muamala da 'yan damfara wadanda suke cewa suna da maganin cutar. Har yanzu a kimiyance ba'a samu maganin cutar ba.
Dangane da hadarin dake tafe da yiwa wadanda suka kamu da cutar jinya a asibitin Yaba ganin yana tsakiyar gari sai Dr Gwarzo yace ai asibitin kato ne kuma an tanadi dakuna na musamman kamar yadda hukumar kiwon lafiya ta duniya ta tsara. Ya kara da cewa wadanda ake yiwa jinya suna samun sauki.
Ana bin digdigin duk dangin wadanda suka kamu da cutar tare da iyalansu da wadanda suke kula dasu. Bugu da kari duk an gaya masu su takaita tafiye-tafiye zuwa wurare. Cutar bata bazuwa ta iska amma attishawa mai karfi ka iya bazata. Haka kuma gawar wanda cutar ta kashe tana da hadari. Tabata kawai na iya sa a kamu da cutar.
Cutar ta samo asali ne a shekarar 1976 daga kasar Zaire ko Kongo kuma a wani kogi mai suna ebola aka fara karo da cutar. Dalilin da yasa aka sama cutar suna ebola ke nan. Amma asalin cutar a cikin dabbobi take kafin ta tsallake ta koma bani Adama kuma wannan shi ne karo na farko da ta bazu barkatai cikin jama'a.
Ga rahoton Ladan Ibrahim Ayawa.