Mai magana da yawun Rundunar sojan Amurka ta Tekun Pacific ya ce makamin ya nuna alamun tarwatsewa ‘yan dakiku bayan harba shi daga mashigen Kalma, a yankin gabashin kasar.
Rundunar sojan Koriya ta arewa ita ma ta ce gwajin bai yi nasara ba.
Kasashen biyu dai basu bada cikakken bayani ko wanne irin makami ne aka gwada ba, kuma dukan su sun ce su na cigaba da yin nazarin gwajin.
A farkon watan nan ne Koriya ta arewa ta harba wasu makaman masu linzami zuwa yankin tekun Japan don maida murtani akan atisayen da dakarun Amurka da na Koriya ta kudu ke yi na shekara-shekara, abinda ita Koriya ta arewa ta dauka a matsayin shirin yaki.
Facebook Forum