Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Guterres Ya Yi Kiran a Samar Da Tsarin Bai Daya Na Rigakafin Coronavirus


Allurar rigakafin coronavirus
Allurar rigakafin coronavirus

Sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira ga manyan kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya, da su kafa wani kwamitin aiki da cikawa wanda zai tsara tare kuma da tafiyar da aikin rigakafin COVID-19 na bai daya a duniya.

"Duniya tana bukatar tsarin rigakafi na kasa da kasa cikin gaggawa don hada duk wadanda ke da sukunin da ake bukata a wuri guda, masu kwarewar kimiyya da masu iya samar da kudade," Abin da Antonio Guterres ya fada kenan a wani babban taro da aka yi ta yanar gizo na Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya game shirin rigakafi na duniya baki daya.

Ya kara da cewa, "Na yi imanin cewa kungiyar G-20 na da sukunin kafa kwamitin aiki da cikawa don shirya irin wannan aikin rigakafin na kasa da kasa da kuma aiwatar da shi da samar da kudade."

Guterres ya ce ya kamata kwamitin aiki da cikawan ya hada da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da Hadin Gwiwar Kasa da Kasa Kan Sha’anin rigakafi (GAVI), da kuma Hadin Kan Duniya game da batun rigakafi COVAX, da duk kasashen da ke da karfin samar da alluran rigakafi ko samar da su idan akwai lasisi.

XS
SM
MD
LG