Gwamnatin kasar Guinea-Conakry ta yanke shawarar gudanar da zaben fitar da gwani na shugaban kasa da aka jima ana dagewa a ranar 7 ga watan Nuwamba. Wani jami’in gwamnatin kasar shi ne ya bayyana wannan cikin daren laraba ta gidan telebijin.
Amma kuma tilas sai shugaban riko na kasar, Janar Sekouba Konate, ya amince da wannan rana kafin a gudanar da zaben. A farkon wannan makon, hukumar zabe ta kasar ta bayar da shawarar gudanar da zaben a ranar 31 ga watan nan na Oktoba, amma kuma gwamnati ba ta amince da hakan ba.
Daga watan Yuli zuwa yanzu, an dage zaben fitar da gwanin na shugaban kasar Guinea har sau hudu a saboda gardamar siyasa, da matsalolin kayan aiki da kuma tashe-tashen hankula masu alaka da zaben.
Za a yi zaben fitar da gwanin ne a tsakanin tsohon firayim minista Cellou Dalien Diallo da dadadden shugaban ‘yan hamayya, Alpha Conde. Wadannan ‘yan takara biyu ne suka fi samun kuri’u a zagayen farko na zaben shugaban kasa da aka yi a watan Yuni.
Wannan shi ne zaben farko da ya kunshi jam’iyyar siyasa fiye da guda a kasar Guinea cikin shekaru hamsin da aka yi ana mulkin kama karya da kuma na soja.