Jam’iyyar dan takarar shugaban kasa Cellou Dalein Diallo a kasar Guinea ta dakatar da shiga aikin kidaya kuri’un da ake yi na zaben fitar da gwani na shugaban kasa wanda aka gudanar a makon da ya shige.
Jiya lahadi, Mr. Diallo yayi barazanar kin yarda da cikakken sakamakon zaben idan har sakamakon ya kunshi kuri’u daga wasu yankuna uku, ciki har da biranen Siguiri da Kouroussa. Dubban ‘yan kabilar Fulani na Mr. Diallo sun bar gidajensu a biranen Siguiri da Kouroussa a sanadin tashin hankalin da ya faru kafin zaben. Jam’iyyar Mr. Diallo ta ce wannan ya rage yawan kuri’un dan takarar nasu, ya kuma hana ‘yan kallon zabe ‘yan kabilar ta Fulani zuwa rumfunan zabe da yawa a yankin.
Har ila yau jam’iyyar ta yi zargin cewa an tabka mummunan magudi a zaben fitar da gwanin, ciki har da kafa rumfunan zabe na karya da cika akwatunan zabe da kuri’u na jebu. A saboda haka ne Mr Diallo yace yana son shugaban hukumar zabe, Siaka Toumany Sangare, ya soke wadannan kuri’un. Amma Sangare yace kotun kolin kasar ita ce ta dace ta takali wannan batun.
Sangare ya ce, "Huukumar zaben ba cibiyar shari’a ba ce, cibiya ce ta aikin da ya shafi mulki. A saboda haka kotun koli ce ya kamata ta takali duk wani korafin da ya shafi zargin aikata magudi."
A yau litinin ake sa ran Sangare zai bayyana wanda ya lashe zaben na fitar da gwani. Mr. Diallo yana son a jinkirta bayyana sakamakon na tsawon makonni biyu, yana mai cewa, "An ga sakamako na rashin kan gado a wannan zaben. Muna da kwakkwarar shaidar da zata nuna an aikata magudi. Guinea ta jira watanni hudu domin gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban kasar, saboda haka zata iya jira na karin makonni biyu kacal domin tabbatar da sahihancin wannan sakamako."
Sakamakon da ake da shi yanzu dai ya ba Mr. Diallo rata 'yar kadan a wannan zaben.