Gwamnatin kasar Guinea ta hana dangin daruruwan mutanen da aka kashe a wata fatattakar ‘yan adawa dake zanga zanga bara, zaman makoki na tunawa da mamatan a daidai inda suka gamu da ajalinsu.
Jiya talata gwamnati ta umarta a rufe kofar shiga babban filin wasan dake Conakry babban birnin kasar domin hana dangin shiga. An yi kananan tarukan tunawa da wadanda suka rasu a majami’ai da masallatai.
Yanzu ya cika shekara guda da ta shige, ne jami’an tsaron kasar Guinea suka bude wuta kan wani gangamin siyasa da ake gudanarwa cikin ruwan sanyi, suka kashe sama da mutane dari da hamsin suka kuma yiwa sama da mata dari fyade.
Ranar Litinin Kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa ta yi kira ga shugabannin kasar Guinea su dauki mataki kan wadanda suka aikata wannan danyen aikin. Kungiyar Human Right Watch ta ce manyan jami’an gwamnati a wancan lokacin ne suka kulla makarkashiyar kai harin, kuma kawo yanzu ba a tuhumi ko mutum guda ba.
Gwamnatin rikon kwarya ta kasar Guinea dake da alhakin shirya komawa mulkin damokaradiya, tayi alkawarin gudanar da cikakken bincike.