Wani bangaren Kungiyar Boko Haran ya sace Leah Sharibu ne tare da wadansu ‘yammata daliban makarantar sakandare ta garin Dapchi su dari da goma ranar goma sha tara ga watan Fabrairu na wannan shekarar aka kuma maido da dari da hudu a watan Maris. Yammatan da aka saki sun bayyana cewa biyar daga cikin daliban sun mutu sabili da wahalar da suka sha lokacin da aka sace su, yayinda kungiyar taki sakin Leah sabili da taki Musulunta.
Gwamnatin tarayyar Najeriya tace ba ta biya ko sisinkwabo ba a matsayin kudin fansa kafin a sako su, bayanan da masu kula da lamura suke tababa a kai.
An dai sace ‘yammatan Dapchin ne kimanin shekaru hudu da sace ‘yammatan sakandaren Chibok dari biyu da saba’in da shida, da har yanzu sama da dari ke hannun kungiyar ba tare da sanin ainihin inda suke ko suna nan da rai ko kuma halin da suke ciki ba.
Saurari cikakken shirin.
Facebook Forum