Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomi Basu Taba Tuntubarmu Ba Tunda Aka Sace Yarmu-Inji Mahaifin Leah Sharibu


Nathanial Sharibu
Nathanial Sharibu

Mahaifin yarinyar nan Leah Sharibu ‘yar shekaru goma sha biyar daya daga cikin dalibai mata dari da goma da aka sace a makarantar Sakandare dake garin Dabchi ranar goma sha tara ga watan Fabrairun wannan shekarar, Nathanial Sharibu, sun bayyana cewa hukumomi basu taba tuntubarshi, ko wani daga cikin iyalinshi ba tunda aka sace ‘yarshi.

A cikin hira da Sashen Hausa bayan fitar da wani faifai da aka yayata ranar litinin da hoton da aka dauka inda aka nuna Leah zaune a kan tabarma tana sanye da hijabi mai ruwa dorowa, mahaifin nata yace babu ko tantama muryar ‘yarshi ce, ya kuma bayyana farincikinsa na jin muryarsa da ta tabbatar da cewa tana da rai kuma cikin koshin lafiya.

Mr. Sharibu ya bayyana cewa ya fara jin labarin faifan daga bakin abokansa, daga nan shima ya shiga yanar gizo ya gani da idonsa ya kuma saurari faifan inda ya tantace cewa, muryar ‘yarsa ce. Yace duk da yake bai ganta da ido ba, jin muryarta kadai ya faranta masa rai domin babbar damuwarsu ita ce sanin lafiyarta. Ya kuma kara jadada kira ga gwamnati ta taimaka ta gaggaguta daukar matakan sakinta.

Da aka tambaye shi bisa ga sanin da ya yi mata, yaya yaji muryarta, sai yace

“Gaskiya ‘yata ce, Leah din ce wannan ‘yata dince, tabbas ita ce, sai dai , kin san inda take akwai wahala ba kamar inda tana hannuna ba. Mai yiwuwa bata samun isasshen abinci a inda take, da sauransu, amma Leah ce, waccan, tabbatacce ‘yata ce wadda tayi magana, hotonta ne, kuma muryarta ce.”

Ya bayyana cewa, a sace Leah tana da shekaru goma sha hudu ta kuma cika shekara goma sha biyar ranar goma sha hudu ga watan biyar. Yace ba daidai bane rahotannin dake cewa shekarunta goma sha bakwai lokacin da aka sace ta. Yace iyalinshi na cikin matukar damuwa dangane da lamarin ya kuma bayyana godiya ga ‘yan Najeriya baki daya da suke addu’a domin Leah yace addu’oi ne ke taimakon iyalin a wannan lokacin. Ya kuma yi kira ga al’umma da su taimaka wajen yin kira da kara matsawa gwamnati lamba a saki Leah ta dawo cikin danginta.

Mr Nathaniel Sharibu ya bayyanan cewa, tunda aka sace ‘yammatan, babu hukuma ko daga matakin karamar hukuma, ko gwamnatin jihar Yobe, ko ta Tarayya da ta tuntubi iyalinsa dangane da batun Leah. Ya bayyana cewa, duk kokarin da ya yi na tuntubar hukuma ko kuma ganawa da wadansu manyan jami’an gwamnati ya cimma tura.

Saurari cikakkar hirar Grace Alheri Abdu da mahaifin Leah Sharibu

Hira da Mahaifin Leah Sharibu-4:45"
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:47 0:00

Wannan ne dai karon farko da aka yi duriyar Leah tun bayanda aka dawo da sauran daliban da aka sace su tare.

Martanin gwamnatin Najeriya

Tun lokacin da aka fitar da wannan faifan dai gwamnatin tarayyar Najeriya bata fita fili tayi wani bayani ba, sai dai kakakin fadar shugaba Buhari Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na twitter cewa gwamnati tana sane da lamarin.

@garbashehu

“We are aware of the audio in circulation concerning the unfortunate situation of our daughter, Leah Sharibu. In dealing with terrorists, nothing is too trivial."

Kakakin shugaban kasar ya kuma bayyana a wani sakon da ya dora a shafin nasa cewa, hukumar tsaro tana gudanar da bincike domin tantance sahihanacin faifan kafin yin tsokaci kan batun.

@garbashehu

“The secret service is analyzing the voice. Our reaction will follow the outcome of the investigation. For President Buhari, nothing will be spared in bringing all our girls home. He will not rest until all of them are freed”

Sace "yan matan Dapchi

Wani bangaren Kungiyar Boko Haram ya sace Leah Sharibu ne tare da wadansu ‘yammata daliban makarantar sakandare ta garin Dapchi su dari da goma ranar goma sha tara ga watan Fabrairu na wannan shekarar aka kuma maido da dari da hudu a watan Maris.

Yammatan da aka saki sun bayyana cewa biyar daga cikin daliban sun mutu sabili da wahalar da suka sha lokacin da aka sace su, yayinda kungiyar taki sakin Leah sabili da taki Musulunta. Gwamnatin tarayyar Najeriya tace ba ta biya ko sisinkwabo ba a matsayin kudin fansa kafin sakin sauran ‘yammatan, ta kuma bayyana cewa tana ci gaba da kokarin ganin an sako Leah.

An dai sace ‘yammatan Dapchin ne kimanin shekaru hudu da sace ‘yammatan sakandaren Chibok dari biyu da saba’in da shida, da har yanzu sama da dari ke hannun kungiyar ba tare da sanin ainihin inda suke ko suna nan da rai ko kuma halin da suke ciki ba.

Sace Yammatan Chibok

Kungiyar Boko Haram ta sace sama da kananan yara dubu daya tunda ta fara tada kayar baya a shekara ta dubu biyu da goma sha uku. Kungiyar ta dauki hankalin kasashen duniya ne a shekara ta dubu biyu da goma sha hudu bayanda ta sace ‘yammatan sakandaren Chibok 276 a jihar Borno cikin watan Aprilu a shekara ta dubu biyu da goma sha hudu.

Kawo yanzu an sami dawo da ‘yammatan Chibok dari da sittin da shida ya hada da dalibai dari da da shida da gwamnatin tarayya ta ceto da kuma sittin da suka tsere da kansu daga hannun kungiyar. An ceto 'yammatan Chibok casa’in da uku lokacin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi musayarsu da kungiyar Boko Haram

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG