Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

GRACE ALHERI ABDU: Domin Iyali, Maris, 22, 2018, Boko Haram Ta Dawo Da Yammatan Dapchi: Kashi Na Daya


Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu

Kungiyar Boko Haram ta saki kusan dukkan yammatan sakandaren Dapchi da ta sace a makarantar Sakandaren Dapchi, ranar da aka cika kwanaki talatin da sace su, yayinda bayyanan da ba a tantance ba ke nuni da cewa, biyar sun rasu a kan hanyar zuwa jejin da aka yi garkuwa da su, kungiyar kuma ta koma da guda daya daga cikin 'yammatan sabili da taki Musulunta.

Wannan na faruwa ne ana saura mako uku a cika shekaru hudu da sace 'yammatan sakandaren Chibok, da har yanzu kungiyar ke rike da dari da goma sha biyu, da babu tabbacin inda suke, ko suna nan da rai duka, ko kuma halin da suke ciki.

Yayinda ake farincikin dawowar 'yammatan, yanayin sace su da yazo daya da yadda aka sace 'yanmatan Chibok, ya zama wani abu da ya haifar da kila wakala, banda haka kuma, tambayar dake zukatan da dama bayan dawo da yammatan Dapchi ita ce , menene ya hana jami'an tsaro kama mayakan bayan sun ajiye 'yammatan?.

Wakilinmu Haruna Dauda Bi'u yayi hira da shugaban kungiyar iyayen yammatan sakandaren Dapchi Bashiru Alhaji Manzo bayan ganawarsu da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari makon da ya gabata.

Bayan samun labarin dawo da 'yammatan, Haruna ya kuma zanta da wani dan jarida da yake cikin ayarin wadanda suka fara isa wurinda aka sauke 'yammatan.

Saurari Cikakken shirin.

Dawo da 'Yammatan Dapchi
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:26 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG