Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iyayen Leah Sharibu Sun Tantance Muryar 'Yarsu


A daren jiya wani kamfanin yada labaran Najeriya ya fidda wata muryar da aka nada a radiyo dake nuna cewa Leah Sharibu, daya daga cikin ‘yan matan makarantar Dapchi da mayakan boko haram suka sace a watan Fabarairu na raye.

Leah na daya daga cikin dalibai mata fiye da 100 da mayakan boko haram suka sace a garin Dapchi dake arewa maso gabashin Nigeria. Mayakan sun saki sauran ‘yan matan amma sun ci gaba da rike Leah, akan cewa ta ki yarda ta musulunta. Iyayen Leah da ‘yan rajin kare hakkokin bil’adama sun ci gaba da yin kiraye kiraye ga gwamnatin kasar akan ta dauki matakin kubutar da ita.

Tun bayan da ‘yan boko haram suka sace Leah, dalibar makarantar sakandaren Najeriya, iyayen ta basu da masaniya ko tana raye ko a’a.

Amma tana yiwuwa sun ji ta karon farko a wata muryar radiyo da aka fidda.

Muryar ta ce nice Leah Sharibu. An sace ni ne daga makarantar Dapchi kuma ina yin kira ga gwamnatin Najeriya ta jikai na.

A daren jiya litinin kamfanin buga labaran na Najeriya, TheCabble ya fitarda muryar da kuma hoton Leah a inda ake garkuwar da ita.

Mahaifin Leah, Nathaniel Sharibu ya shaida cewa muryar diyarsa ce.

“Mr. Sharibu ya ce Ita ce. Tabbas Ita ce. Na sami kwarin gwiwa sosai jiya da na ji muryarta. Yanzu na yi imani diyata na raye.

A cikin wani faifan sauti mai dauke da muryar wanda ake zaton Sharibu ce, ta yi kira ga gwamantin Najeriya ta taimakawa iyalanta, saboda suna cikin mawuyacin hali tsawon watannin da yan Boko Haram suka sace ta tare da sauran dalibai su dari.

Yan bindigar sun sako sauran daliban, amma har iyau ita Sharibu tana hannunsu, saboda taki karban addinin Musulunci kamar yanda rahotanni suka bayyana.

Sakon take na a saki Leah Sharibu da wannan faifan, na ci gaba da bazuwa ta shafukan sada zumunta a Najeriya

Wata yar fafutuka a Najeriya Rebecca Gdzama, tace bayyanar wannan faifan na nuna Allah na karban addu’o’I da ake yi. Tace "Na san wannan lamari zai taso wata rana. Ina da imanin cewa gwamnatin ta himmantu ta kwato wannan yarinyar, don haka na dade bani da shakku."

Gwamnatin Najeriya bata tantance ingancin wannan faifan nan da na ba. Mai Magana da yawun shugaba Muhammadu Buhari yace suna gudanar da bincike a kan wannan faifan.

Kungiyar rajin kwato yan matan Chibok ta Bring Back Our Girls, da aka kafata bayan Boko Haram ta sace yan matan makaranta 2014, ta lashi takobin kara matsin lamba a kan gwamnati domin sako Sharibu. Daya daya cikin 'yan fafatukar Mannasseh ya bayyana dalilinsa na neman ganin hoton bidiyon.

"Abin da yasa nake so in kalli hoton bidiyon saboda mu ga yanda lafiyarta yake. Ina son inga bidiyo na tsarin sako ta. Me suke nema su sako ta. Su fito su bayyana mana abin da suke ayi musaya da su a karbo Leah. Kudi ne? Ko kuwa dai mayakansu da aka kama a baya, ko dai wani takamaimai suke so? Idan har da gaske gwamnati take yi, zata iya karbo wannan yariya tsakanin sa’ao’I 24"

Gwamnatin Najeriya ta sha suka mai yawa a kan tsawon loakcin da ya dauketa ta kwato yan matan makarantar Chibok 276 da Boko Haram suka sace su. A shekarar da ta gabata an sako yan matan 89 a cikin wata musayar da gwamnati ta yi mayakan Boko Haram dake daure gidan yari, amma kuma har yanzu akwai yan matan sama da dari da ba a gansu ba, amma dai ana kyautata zato suna hannun yan Bindigar.

Kungiyoyin rajin kare hakkin bil adama sun ce Boko Haram ta sace akalla yara dubu biyu tun cikin shelarar 2009, lokacin da ta fara da sunan kafa Musulunci.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG