Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya Ta Kudu Da Ta Arewa Na Kokarin Tattaunawa Da Hada Kan Iyali


Koriya ta kudu da takwararta Koriya arewa sun fara yunkurin samar da wani sabon shiri domin inganta zaman lafiya da kwamciyar hankali da kuma hada kawunan iyalai tsakanin kasashen biyu.

A yau Litinin Koriya ta Kudu ta samar da wani shirin tattaunawa da kuma sake hada iyalai da Koriya ta Arewa, domin neman hanyar kawo kwanciyar hankali tsakanin kasashen biyu bayan da Koriya ta Arewa ta ci gaba da shirinta na makaman Nukiliya da masu Linzami.

A cewar mataimakin Ministan tsaro na Koriya ta Kudu, Seo Joo-seok, “Ma’aikatar tsaro ta shirya wani zaman tattaunawa tsakanin Koriyoyin biyu a ranar 21 ga wannan wata, a garin Tengilgak dake Koriya ta Arewa, domin dakatar da duk wasu ayyuka dake kawo zaman ‘dar ‘dar tsakanin kasashen.”

Tongilgak wani gini ne mallakar Koriya ta Arewa a garin Panmumjom dake kan iyaka, da aka taba gudanar da irin wannan zaman tattaunawar a baya.

Tun lokacin da shugaba Moon Jae-in ya zama shugaban kasar Koriya ta Kudu a watan Mayu, gwamnatinsa ke kokarin shawo kan Koriya ta Arewa ta saukaka shirinta, ciki harda tayin bada taimakon gaggawa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG