Da alamar sojojin Iraki za su yi amfani da wata damar da ta samu, ta barkewar rikice-rikice a shugabancin gyauron kungiyar ISIS mai cike da rauni, su kai ma kungiyar farmaki ta fagage daban-daban su kawar da ita.
Amma wannan dabarar ka iya zama mai hadari ganin irin asarar rayukan da sojojin na Iraki su ka yi yayin kokarin sake kwato birnin Mosul.
Ma'aikatar Tsaron Amurka ta yi kiyasin cewa mayakan ISIS sun hallaka kashi 40% na sojojin Iraki na musamman a tsawon watannin taran da su ka yi na gwagwarmayar sake kwato birnin. Kuma Kwamandan hadakar kasa da kasa ta yaki da kungiyar ISIS na bangaren Amurka ya ce, "yakin birnin Mosul ne mafi muni da tsanani da na taba gani rayuwa ta."
To amma wasu jami'an sojojin Iraki da su ka kawo ziyara a Ma'aikatar Tsaron ta Pentagon a wannan satin, bayan shelar nasara kan ISIS da aka yi a birnin Mosul, sun nuna alamar gabansu gadi game da shirin.
"Kwanan nan, za mu fara wani aikin soji na kwato sauran yankunan Iraki da har yanzu ke karkashin mamaya," a cewar mai magana da yawun Rundunar Hadin Gwiwa, Burgediya Yahaya Rasul.
Facebook Forum