Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobara Ta Kashe Sama Da Mutun 100 a Wurin Wani Taron Daurin Aure a Iraqi


Iraqi
Iraqi

Wata gobara da ta tashi a wani daki da ake taron daurin aure a Arewacin Iraqi ta yi sanadin mutuwar sama da mutane 100 sannan wasu 150 sun jikkata a ranar Laraba, inda hukumomin suka yi gargadin yiwuwar karuwar alkaluman mace-macen.

Gobarar ta tashi ne a lardin Nineveh na kasar Iraki a yankin Hamdaniya, a cewar hukumomi, mafi akasarin mazauna yankin Kristoci ne dake zama a wajen birnin Mosul mai tazarar kilomita 335 a arewa maso yammacin babban birnin kasar Baghdad.

Wasu bidiyo da aka nuna ta kafar talabijin sun nuna yadda wutar ta yi ta ci yayin da ta karade dakin da ake daurin auren. Bayan an kashe gobarar kuma, babu abinda ya rage illa baraguzan karahunan da suka kone.

An garzaya da wadanda suka tsira zuwa asibitocin yankin, inda aka sanya musu iskar oxygen sannan kuma aka daura musu bandeji a raunukan da suka ji, yayin da iyalansu suka yi ta kai da komo a ciki da farfajiyar asibitin su kuma ma’aikatan jinya suka yi ta kokarin tanadar karin iskar oxygen.

An fara kokarin ganin cewa an tallafa wa wadanda al'amarin ya auku da su a mummunar gobarar da ta yi barna sosai, a cewar Saif al-Badr.

Firai Ministan kasar Mohammad Shia al-Sudan, ya ba da umarnin a kaddamar da bincike domin gano musabbabin gobarar sannan ya umarci jami'an hukumar lafiya da na ma'aikatar cikin gida da su ba da agajin jinkai, a cewar ofishin a wata sanarwa da aka fidda ta yanar gizo.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG