Ruwa ya lashe mutane akalla 113 a sanadin mummunar igiyar ruwan da ta biyo bayan girgizar kasa mai karfi a Indonesiya, yayin da amon wutar da wani dutse yayi ya kashe wasu mutanen su 18.
Igiyar ruwan da tudunta ya kai mita uku a wasu wuraren ta bugi gabar Sumatra, a bayan da girgizar kasa mai karfin awu 7.7 ta abku, kimanin kilomita 20 a karkashin kasa daga can kasa da teku a cikin daren litinin. Masu aikin ceto su na neman mutane har 500 wadanda har yanzu ba a san inda suke ba.
Jiya talata a tsakiyar tsibirin Java, Dutsen Merapi yayi amon wuta, ya cilla toka mai tsananin zafi sama, narkakken dutse kuma ya malala kasa, a bayan da yayi kwana da kwanaki yana gurnani. Wasu mutanen kauyukan dake dab da wannan dutsen da yayi amon wuta sun kone kurmus a saboda ba su bar kauyukan kamar yadda hukumomi suka umurce su ba.
Shugaba Barack Obama na Amurka da mai dakinsa Michelle sun bayyana jimaminsu da hasarar rayuka da kuma raunukan da aka ji a sanadin girgizar kasa da kuma mummunar igiyar ruwan da ta haddasa. Sanarwar da suka bayar jiya talata ta yi alkawarin cewa Amurka zata taimakawa al'ummar kasar Indonesiya.