A lokacin bazara, wa'adin nasa zai kare Tottenham.
A dai watan Satumbar bara, Bale mai shekara 31 ya koma Tottenham a matsayin aro karkashin wani kwantiragi na tsawon kakar wasa daya.
A baya, an yi ta hasashen yadda makomarsa za ta kasance, amma a ranar Talata sai ga shi ya fito yana cewa yana fatan zai koma Real Madrid don buga kakar wasa ta 2021-2022, kamar yadda kafafen yada labarai suka ruwaito
A watan Yunin 2022 kwantiragin Bale zai kare a Madrid, amma al’amuransa sun dagule a kungiyar ta Spaniya.
Duk da ya zura kwallo sama da 100, ya kuma lashe kofin La Liga biyu da na Champions League hudu – da kuma fitacciyar kwallon nan da ya ci Liverpool a shekarar 2018, Bale ya fuskanci kalubale a zamansa da Madrid.
Ya sha fuskantar suka daga masoya kungiyar ta Madrid, sannan a karshen kakar wasa ta 2018-2019, manajan kungiyar Zinadine Zidane ya taba cewa, zai fi kyau idan Madrid ta raba gari da Bale.
Wata tuta da Bale a rike a shekarar 2019 a lokacin yana bugawa Wales wasa, dauke da wasu kalmomi “Wales. Golf. Madrid,” sun bakantawa mutane rai da dama.