Tun bayan da aka fitar da jerin sunayen kungiyoyin da za su kara a wasannin quarter-final da semi-final a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai ta UEFA, aka tayar wa da masu sharhi da masoya kwallon kafa tsimi.
Jama’a dai na ta tsokaci kan yadda wadannan wasannin za su kaya wadanda za a yi su a watan Afrilu mai zuwa.
A ranar Juma’a aka fitar da sunayen kungiyoyi takwas, uku daga Premier League, biyu daga gasa Bundesliga, daya daga gasar Faransa ta Ligue 1 sai daya daga gasar La Liga da FC Porto ta Portugal.
Karin bayani akan: UEFA, Bundesliga, Real Madrid, Liverpool, PSG, Manchester City da gasar Premier.
Ga yadda aka tsara karawar kungiyoyin a Quarter Final:
Manchester City vs Borussia Dortmund
FC Porto vs Chelsea
Bayern Munich vs Paris Saint-Germaine
Wannan hadi ya sa jaruman gasar Premier Manchester City za su yi gaba da gaba da Borussia Dortmund – daya daga cikin wasannin da ake ganin za a yi kare-jini-biri-jini.
Bayern wacce ke rike da kofin gasar, ita ta doke PSG da ci 1-0 Lisbon inda suka lashe kofin gasar na bara.
Wani wasa kuma da zai dau hankalin masoya kwallon kafa shi ne tsakanin Liverpool da Real Madrid wadanda rabon da su hadu a tun a shekarar 2018.
A ranar 29 ga watan Mayu za a buga wasan karshe a birnin Istanbul na kasar Turkiya.