Mai horar da ‘yan wasan kungiyar kasar Janne Andersson ne ya bayyana hakan a wani jawabi da ya yi daga birnin Stockholm yayin yake fitar da jerin sunayen ‘yan wasan kasar.
Hakan na faruwa ne yayin da kasar ke shirin karawa a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya inda za su kara da Georgia a ranar 25 ga watan Maris da kuma karawar da za su yi da Kosovo kwana uku bayan wasansu da Georgia.
Sannan Sweden din za ta kara a wasan sada zumunci da Estonia a ranar 31 ga watan Maris.
Kwallaye 62 Zlatan dan shekara 39, ya taba ci wa kasarsa cikin wasanni 112 da ya buga mata a tsakanin shekarun 2001 zuwa 2016.
Ibrahimovic wanda ke bugawa AC Milan ta kasar Italiya wasa, ya shiga shafinsa na Twitter a ranar Talata inda ya bayyana shirinsa na komawa fagen wasan kasa da kasa.
Hakan na nufin, shi ne dan wasa mafi yawan shekaru da zai bugawa Sweden kwallo.
Hukumomin kwallon kafar kasar sun kwatanta Ibrahimovic a matsayin kwararren dan wasan da Sweden ba ta taba samun irinsa ba.
Tauraron Ibrahimovic ya kasance yana haskawa a wannan kakar wasa, inda ya zura kwallo 16 a wasa 21 ga kungiyarsa ta AC Milan a gasar Seria A ta kasar Italiya.
Andersson ya yi lale marhabin da yadda Ibrahimovic ya nuna sha’awarsa ta sake yi wa kasarsa hidima.