Mutanen dai na rike da alluna dake dauke bukatunsu wanda ke cewa ‘yan Majalisar su bayyana kasafin kudinsu domin jama’a su sani, tare da gudanar da bincike kan zarge zargen cin hanci da rashawa dake kara yawa a kasar.
Efe Williams, shine ya wakilci kungiyar Foundation against Corruption a gangamin yace suna da bukatun da suke nema gurin ‘yan Majalisa, na farko shine abude takardun ‘yan Majalisun kowa yasan menene yake ciki, na biyu shine dalilin da yasa suka ki amincewa da zuba kudi a asusun banki, na uku a raba kudaden kananan hukumomi da na jihiho daban daban, na hudu hukuncin kisa ga duk wanda yaci hanci da rashawa, na biyar ‘Yan Majalisa su rage kudin da ake biyansu da kaso 70 cikin 100.
Masu gamgamin dai sunce yanzu ne suka fara zaman dirshan a kofar Majalisa, har sai baba ya gani, domin tabbatar da an dauki mataki akan bukatun na su, kamar yadda Hawwa Adam ta bayyana, inda tace suna bukatar ‘yan Majalisun su amince da barin shugaban kasa yayi aiki yadda komai zai yalwata a Najeriya.
Shi kuma kwamarad Ibrahim Sani Bello, cewa yayi yawancin kasashe sun ci gaba ne da ire iren wadannan gwawarmayar da suke yi yanzu haka a kofar Majalisa. Domin wadanda ke sama basa kallon na kasa har sai na kasan sun nuna cewa sun san ‘yancin su.
Ya zuwa yanzu dai jami’an tsaro sunyi dafifi a kofar Majalisar, haka kuma babu wani jigo da ya fito domin karbar takardar jawabin masu gangamin.
Domin karin bayani.