A cewar majalisar yanzu kimanin shekara daya ke nan da gwamnatin jihar bata bata ko kwandala ba na yiwa mazabu aiki kamar yadda doka ta tanada.
A cikin kundun tsarin mulkin kasar Najeriya kowane dan majalisa ya kamata gwamnati ta bashi nera miliyan goma sha biyar kowane watanni hudu ko kuma nera miliyan arba'in da biyar a shekara. Kudaden na ayyukan raya kasa ne a mazabunsu. Inji 'yan majalisar basu kudin doka ce domin yana cikin kasafin kudin shekarar 2016 wadda suka sanyawa hannu.
Shugaban kwamitin kula da harkokin ma'aikata na majalisar dokokin Onarebul Abdulmalik Madaki Boso ya kira taron manema labarai domin bayyanawa duniya halin da suke ciki. Yace daga watan Janairu zuwa wannan watan ya kamata a ce an basu sau uku ko.
Shi ma shugaban marasa rinjaye na majalisar Onarebul Bello Agwara yace hujjar da gwamnati ta bayar basu gamsu da ita ba. Yace sun sha zuwa su zauna da gwamnan su yi magana dashi cikin laluma tare da nuna masa kudin hakkinsu ne. Amma sai yace masu babu kudi saboda haka su koma su bayyanawa mutanensu. Yace basu gamsu da bayanin gwamnan ba domin sun ga ana harkoki da kudi.
Gwamnatin ta sake jaddada cewa rashin kudi ne ya sa ba'a ba 'yan majalisar kudaden ba tare da kiransu su kara hakuri. Kwamishanan labaran jihar Mr. Jonathan Batsa shi ya mayar da martani a madadain gwamnati.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.