Taron ya hada da jami'an tsaron soja da na 'yanasanda da jami'an tsaron farin kaya wato DSS da jami'an Civil Defence da hukumomin shige da fice da na Road Safety da kungiyar matasan sa kai da aka sani da Civilian JTF har da ma jami'an gidan yari.
Duk wadannan an tarasu ne domin su bada tasu gudummawa akan hanyoyin da za'a iya bi domin kawo karshen irin ta'adanci da ya addabi yankin arewa maso gabas tare da yadda za'a tallafawa wadanda suka tuba domin kada su koma jidan jiya.
A wurin taron an baiwa mutane daman tofa albarkacin bakinsu walau a rubuce ko kuma ta hanyar yin bayanai. Nan take jama'a da dama suka dinga yin bayanan irin matsalolin da suke fuskanta musamman dangane da irin kananan hare-haren da ake kaiwa mutanen dake kauyuka kuma har yanzu suna faruwa.
Shugaban taron Mr. Julius Dan Asabe Yakubu yace dama dalilin taron ke nan domin a samun gudummawar jama'a domin mahukunta su san abubuwan dake faruwa kana su san matakan da zasu dauka.
Baicin jami'an tsaro akwai sarakunan gargajiya da shugabannin addinai da suka halarci taron. Wani yace matsalar tsaro a kauyuka ta fi karfin gwamnati su kadai. Sun kira sojoji su dinga yin anfani da abun da jama'a ke fada masu akan lamuran dake gudana musamman a kauyuka domin da zara an fita daga birni cikin tafiyar mil biyu ko uku za'a sami 'yan ta'ada.
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.