Kwamishinan ma’aikatar kiwon lafiya na jihar Borno, Dakta Haruna Mshelia, ya shedawa manema labarai cewa, ana da sansanin yan gudun hijira kusan 28 kuma an sami mace macen kananan yara a cikin wadannan sansanin.
Yanzu haka dai gwamnati da dauki wani mataki da kuma wasu kungiyoyi masu zaman kansu wanda ke tallafawa irin wadannan kanan yaran dake da shekaru biyar zuwa kasa, da kayayyakin abinci masu gina jiki da magunguna har ma da rigakafi.
Dakta Mshelia, yace an sami sabani wajen rahotannin da wasu kafafen yada labarai suka dauka na cewa cutar yunwa ce ta kashe kananan yaran, yace ba yunwa bace kadai har ma akwai zazzabin cizon Sauro da ciwon amai da gudawa da cutar limoniya da cutar Kyanda da dai sauran wasu cututtuka na daban.
Domin karin bayani.