Wasu yan jam’iyyar kuma na zargin cewar da hannun sakataren gwamnatin tarayya Mr Bidi Lawal, a wannan rikicin, batun da suka ce bazasu amince ba, su kuwa ‘yan ‘daya bangaren na musunta wannan zargi.
Hon Usaini Gambo Bello, dake zama shugaban yan shinkafa na Jam’iyyar yace bazata sabu ba bindiga a ruwa, yakuma zargi wasu manyan da suke sama da cewar sune ke lalata lamarin, domin wasu na da kishin jihar Adamawa, wasu kuwa basu da shi.
Shugaban rikon kwamitin da aka kafa Hon Ibrahim Bilal, ya musunta wannan zargi inda yace sun zone domin suyi gyara.
Amma wasu yan Jam’iyyar sun fara gargadin gwamnan jihar Sanata Bindo Umaru Jibrilla, da ya tsome hannunsa a wannan rikici da ke faruwa yanzu a jihar.
Yanzu haka dai lokaci ne kan iya tabbatarwa da yadda zata kasance yayin da iyalan gidan siyasar Murtala Nyako ke kada gangan zuwa kotin koli.
Domin karin bayani.