Firayim Ministan Birtaniya David Cameron ya ci alwashin murkushe kungiyar ISIL bayanda wani ma’aikaci dan kasar Birtaniya ya zamo mutum na uku da kungiyar mayakan ta datsewa kai.
Mr. Cameron ya bayyana jiya lahadi cewa, kisan rashin imani ne. Yace mayakan kungiyar masu da’awar daular Musulunci ba Musulmi bane, shaidanu ne, ya kuma yi alkawarin yin farautar wadanda suka kashe dan asalin Birtaniya ko ba jima-ko ba dade.
Hoton bidiyon kisan David Haines dakungiyar mayakan ISIL ta sa a yanar gizo ranar asabar ya yi kama da hotunan bidiyon datse kawunan ‘yan jarida Amurkawa biyu-James Foley da Steven Sotloff da kungiyar ta yayata. An nuna Haines a durkushe cikin Hamada yayinda wani mutum sanye da taguwar mayaka data rufe kai da fuskarsa ya yi magana da harshen Birtaniya cewa ramuwar gayya ce sabili da hada hannu da Amurka da Mr. Cameron ya yi.
An kuma nuna wani mutum shima dan asalin kasar Birtaniya da mai kisan, yace, shima za a kashe shi.
Shugaban Amurka Barack Obama ya bayyana kisan Haines a matsayin rashin imani, ya kuma ce Amurka zata yi tafiya kafada da kafada da Birtaniya wajen jimamin kashe mutanen da kuma shawo kan kungiyar