Kudurin da shugaban Amurka Barack Obama ya gabatar kan shirinsa na murkushe kungiyar ‘yan ta’adda da ake kira ISIS a Iraqi da Syria ya janyo martini daban daban daga wakilan majalisar dokokin Amurka.
Kakakin majalisar wakilai ta Amurka John Boehner daga jihar Ohio ya fada jiya Alhamis cewa, galibin ‘yan majalisar na jam’iyyar Republican basa jin shirin na shugaban Amurka da ya gabatarwa kasar ranar Laraba zai yi tasiri wajen murkushe kungiyar ISIS. Mr. Boehner ya kara da cewa ‘yan Republican masu yawa suna tunanin akwai bukatar daukan Karin matakai kan kungiyar.
Wakili John Fleming daga jihar Lousiana ya kira shirin na shugaban kasa “rudadden shiri” da zai bukaci Amurka ta dogara kan mutane da suka nuna cewa ba za’a iya amincewa dasu ba wajen yakar kungiyar ISIS.
Amma dan majalisa Eliot Engel dan jam’iyyar Democrat yace daga New York ya gayawa majalisar cewa yana goyon bayan shirin na Mr. Obama sosai, ya kara da cewa matakin na yanzu ai somin tabi ne.
Ahalinda ake ciki kuma sakataren harkokin wajen Amnurka John Kerry ya yi watsi da da ikirarin Rasha cewa matakan soja da Amurka zata dauka kan kungiyar ISIS na gaban kanta ne kuma hakan ya kaucewa dokokin kasa da kasa.
Mr. Kerry wanda yayi magana da manema labarai wadanda suke rangadi tare da shi a Saudi Arabiya yace kusan abun dariya ne a ji Rasha ganin irin take takenta a gabashin Ukraine da kuma kama yankin Crimea tana maganan dokokin kasa da kasa ko Majalisar Dinkin Duniya.