Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabuwar Daular Islama Tana Yiwa Zaman Lafiyar Duniya Barazana


Sakataren tsaroon kasar Amurka Chuck Hagel
Sakataren tsaroon kasar Amurka Chuck Hagel

Sakataren harkokin tsaron Amurka Chuck Hagel yace Daular Islama da ta kwace wasu sassan kasashen Iraqi da Syriya tana yiwa zaman lafiyar duniya barazana fiye da yadda ake zato

Sakataren Tsaron Amurka Chuck Hagel ya ce barazanar da masu tsattsauran ra'ayi na Daular Islama ke wa tsaron duniya baki daya, ya wuce duk wani abin da aka taba gani.

Da ya ke jawabi a jiya Alhamis a birnin Washington, Hagel ya bayyana 'yan bindigar da cewa kungiya ce da ta zarce ta 'yan ta'adda na yau da kullum. Ya ce kungiyar ta fi duk wata kungiyar ta'addanci da aka taba yi makamai da dabarun yaki da kuma kudi.

"Su na matukar barazana ga duk wani muradinmu, walau a Iraki ko ma a duk wani wuri." inji shi.

Hagel na jawabin ne ganga da Hafsan Hafsoshin Amurka, Janar Martin Dempsey, wanda ya bayyana kungiyar ta Daular Islama da cewa "su na da hankoro salon na karshen duniya."

Janar din ya ce za a iya cin kungiyar da yaki, to amma sai idan an far ma ta a Syria da Iraki. Ya yi hasashen cewa za a iya kawar da al'adar gwagwarmaya da makami ce kawai idan mutanen yankin masu yawan miliyan 20 da ke takure a wannan babban yankin, tun daga birnin Damascus zuwa birnin Bagadaza.

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG