Taron da aka gudanar da hadin gwiwar jami’an tsaro ya hada kan shugabannin al’umomin Berom da Irigwe da a makon jiya suka sami matsala har ya kai ga rasa rayukan mutane 10.
Shugaban karamar hukumar Jos ta Kudu, Augustine Pwakim, yace domin kare rayukan mutane daga salwanta yasa suka hadu da matasa da gwamnati da kuma hukumomin tsaro. Haka kuma zasu ci gaba da tattaunawa da matasa domin samar da zaman lafiya.
Kwamandan rundunar tsaro ta Special Task Force a jihar Filato, Janal Nicolas Rogers, yace taron na neman mafita ne daga rikice-rikecen da ke faruwa, hakan yasa suke gudanar da taruka tsakanin mutanen da abin ya shafi don ganin hakan bata kara faruwa ba.
Domin karin bayani saurari rahotan Zainab Babaji.