Masu zanga zangar da bangare daya na caccakar gwamnatin Buhari daya kuma na marawa gwamnatin baya suna daga murya suna fadan abun da suka fito cimma a Abuja.
Jigogi a cikin zanga zangar 'yan kungiyar ceto 'yan matan Chibok ne da aka fi sani da suna Bring Back Our Girls ko BBOG a takaice kaman su Maureen Kaburuk da Fatima Abba Kaka.
Fatima Kaka tace 2Face wanda yayi ikirarin shirya gangamin daga baya kuma ya janye tace ba shi ba ne jagoran gangamin tun can ainihi. Mutane da yawa suka zauna suka yadda su yi gangamin domin abun ya isa haka nan.
Maureen Kaburuk na korafin shugaba Buhari baya fayyace bayani kan muradun gwamnatinsa. Wai sai ya fita kasar waje idan an tambayeshi kana yake bayyana abubuwan da gwamnatinsa keyi a Najeriya. Tace amma idan yana gida Najeriya shuru ka keji kamar an shuka dusa.
Maureen Kaburuk ta cigaba da cewa su ne suka fito suka zabi Shugaba Muhammad Buhari. Tace ranar zabe tana ofishin hukumar zabe ta kasa har zuwa karfe ukku na dare domin tabbatar an fitar da sakamakon zaben na zahiri. Tace saboda haka suna da 'yancin su fito suyi magana idan gwamnati na wani abun da basu ji dadinsa ba.
Abdulhamid Dankirko na bangaren masu marawa Shugaba Buhari baya. Yace Allah ya taimaki Buhari ya kawowa kasar tsaro. Yace babu abun da mutum zai yi idan babu tsaro. Yace su suna goyon bayan Shugaba Muhammad Buhari saboda mutum ne mai gaskiya, mai rikon amana, mai tabbatar cewa kowane dan Najeriya an saurareshi kuma ya fadi matsalolinsa.
Bangarorin biyu dake zanga zanga sun yi maci har kofar fadar shugaban kasa ba tare da wata tsangwama ba, ba kuma tare da wani ya yakushi wani ba, kuma 'yansanda sun yi dafifi domin tabbatar da doka da oda.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.