Wani Muhammad Abubakar wanda yake karamar hukumar Potiskum yace tun watan Satumbar shekarar 2015 aka dakatar da albashinsu kuma su basu san dalilin yin hakan ba.
To saidai gwamnati ta tura kwamitin tantancewar zuwa Potiskum inda ya shaida masu cewa su ma'aikata ne amma gwamnati bata da kudin da zata biyasu. An gaya masu dole za'a rage wasu a kuma biya wasu.
Sun kira gwamnan Yobe ya duba Allah, ya ji tsoronsa domin hakkinsu yana kansa. Idan gwamnan bai yi masu ba gobe kiyauma Allah zai tambayeshi.
Shi ma wani malam Mari yace yau fiye da shekara daya bashi da albashi. Yana da iyalai kuma dole ya biya kudin makarantar yara. Yace sai wanda ya iya fadanci ake biya.
Shugaban kungiyar ma'aikatan jihar Musa Hassan El-Badawi yace suna sane da halin da ma'aikatan suke ciki. Yace wadanda basu san hawa ba balantana sauka ba aka cutar dasu ba bisa laifinsu ba. Yace kwamitoci sun kai hudu ko biyar amma babu gaskiya a cikin ayyukansu. Zalunci ake yiwa mutane.
Amma gwamnatin jihar tace a iyakacin saninta bata da matsala da biyan albashin ma'aikatanta na kananan hukumomi.
Kwamishanan yada labarai na jihar yace sun gama tantancewa kuma duk wanda bashi da matsala an biya albashinsa.
Ga rahotn Hassan Maina Kaina da karin bayani.