A cewar kakakin rundunar STF Manjo Adam Umar, maharan sun kashe mutane 21 a kauyen, kuma harin ya zo ne bayan wasu tarurrukan samar da zaman lafiya da rundunar Operation Safe Haven ta yi tsakanin mutanen Iregwe da Fulanin yankin.
Domin tabbatar da zaman lafiya a yankin rundunar sojan Najeriya ta kara yawan sojojinta a yankin.
Da yake karin haske akan wani rikici da ya barke, Manjo Adam ya ce wasu mahara ne da ba a tantance inda suka fito ba, suka kai wani kauye da ke bayan gari inda suka harbi mata guda hudu kafin su bar wurin.
Kwana guda bayan afkuwar wannnan lamari, samari suka fito suna gudanar da zanga-zanga, har ta kai ga arangama da abokan zamansu Fulani.
Daya daga cikin shugabannin al'uma a karamar hukumar Bokkos, Ayuba Matawal, ya ce ya zuwa yanzu fiye da mutane 25 ne suka mutu, da yawa kuma suna gudun hijira.
Kwamishinan yada labaran jihar Filato, Yakubu Datti, ya ce gwamnati na ci gaba da hada kai da jami’an tsaron jihar don kawo karshen tashin hankalin da ya addabi jihar.
Domin karin bayani saurari rahotan Zainab Babaji:
Facebook Forum