Hukumar kwastan mai kula da jihohin Oyo da Osun ta kama buhuhuwan shinkafa, tsoffin tayoyi, dilolin kawanjo da man girki da aka kiyasata kudinsu ya dara Nera miliyan tasa'in.
Alhaji Tanko Bayero Muhammad shi ne mataimakin kwanturolan kwastan dake kula da jihohin Oyo da Osun ya yiwa Muryar Amurka bayanin abun da suka kama. A cewarsa "Mun kama trucks na shinkafa guda tara. Mun kama jarkunan man gyada sun kai fiye da hamsin. Mun kama used tires da yawa. Sannan mun kama gwanjo, su ma gasu nan bails and bails".
Inji Alhaji Tanko Bayero Muhammad bisa ga nasu lissafin kudaden kayan sun kama N92, 778, 048. 22. Sun kama kayan ne a wata karamar hukumar Iwajowa cikin jihar Oyo.
Kamar yadda hukumar kwastan take da masu bata bayanan sirri, su ma 'yan sumoga suna da masu basu bayani, saboda haka kayan suka samu kamawa tare da direba daya amma duk sauran sun yi ta kare inji Alhaji Tanko.
Ga rahoton Umar Hassan Tambuwal da karin bayani.
Facebook Forum