Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jajanta wa ‘yan Najeriya kan wahalhalun da suke fuskanta sanadiyar matsalar karancin mai da kasar ke fuskanta.
Buhari ya nuna taikaicinsa ne a wata rubutacciyar sanarawa da Fadar Shugaban kasar ta fitar a yau Lahadi wacce Muryar Amurka ta samu.
“Ina mai jajinta wa duk ‘yan Najeriya, saboda wahalar da suke fuskanta ta bin dogayen layukan mai.” Sanarwar ta bayyana.
Shugaban na Najeriya ya ce ana kan sanar da shi halin da ake ciki musamman kan irin matakan da matatar man fetir din kasar ta NNPC ke dauka na kawo karshen matsalar.
“Na samu tabbaci daga kamfanin NNPC cewa, komai zai daidaitu nan da wasu ‘yan kwanaki masu zuwa, saboda ana kan raba man.” sanarwar ta ce atre da ba 'yan Najeriya hakuri.
Buhari ya ce ya kuma ba masu ruwa da tsaki umurnin su kara kaimi wajen sa ido tare da yaki da masu boye man, a kuma dakile hauhawan farashinsa.
“Ina mai baku tabbacin cewa hukumomin da ke da alhaki za su ci gaba da samar da sabbin bayanai kan wannan matsala.” Sanarwar ta kara da cewa.
Facebook Forum