Shugaba Buhari ya kwashi watanni biyu kenan yana mulki ba tare da majalisar gudanarwa ba duk da cewa daga dukan alamu ya bi doka wajen fitar da minista guda daga kowace jiha kamar yadda sashi na 147 na kundin tsarin mulkin kasa ya tanada amma kuma bai hado su da sunaye ma'aikatu da za su yi aiki ba.
Wani Kwararre a bitar kundin tsarin mulki Barista Mainasara Kogo Ibrahim yace kundin tsarin mulki bai yi bayani a kan dole sai an hada su da ma'aikatun su ba, kawai kundin tsarin mulki yace dole ne a samu wakili daga ko wace jiha kuma shugaban kasa na iya amfani da huruminsa ya nada su yadda yake so.
Tsohon Ministan Albarkatun Ruwa na Kasa Suleiman Aadam na cikin wadanda aka tantance kuma yace ya gamsu da irin tambayoyin da akai masa, ko da yake yace ba a barshi yayi wasu bayanai ba da yake ganin zasu iya taimakawa majalisar wajen rubuta rahottanin ta.
Shima Sanata Mohammed Ibrahim Bomoi yace sai majalisa ta gama tantance ministocin kafin shugaba Buhari ya basu ma'aikatu da ya dace da su ta rahoton da majalisa za ta rubuta masa.
An riga an tantance ministoci 40 a cikin 43 da aka aika dasunayen su wa Majalisar Dattawan.
Ga rahoton Medina Dauda a kan wannan batu:
Facebook Forum