Shugaba Muhammadu Buhari ta bakin kakakinsa Mallam Garba Shehu, ya ce, ba Shi'a ne aka haramta ba, a'a, kungiyar IMN ta Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, wanda yanzu ya ke tsare ne aka haramta.
Game da batun sulhu kuwa, kakakin na shugaban kasa, ya ce, tuni gwamnatin ta bude kofar sulhu.
To sai dai kuma a martanin kungiyar ta IMN ta bakin kakakinta Mallam Ibrahim Musa, ta ce zata dau mataki kan wannan umarni da kotu ta baiwa gwamnatin Najeriya, kan kungiyar ta ‘yan uwa Musulmin.
Masana harkar shari’a suma sun soma fashin baki, Barr. Bello Ibrahim Jahun, malami ne a tsangayar koyon aikin shari'a a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria, ya bayyana makomar wannan umarni a fagen shari'a.
Suma kungiyoyin kare hakkin bil adama, irinsu Amnesty Support Group, na ganin hawa teburin sulhu shine mafita, Mallam Musa Jika na cikin shugabanin kungiyar.
Ga cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdul'aziz cikin sauti.
Facebook Forum