Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa Za Ta Fara Janye Dakarunta Daga Nijar A Wannan Makon


Dakarun Faransa A Sansanin Sojan Ouallam A Nijar
Dakarun Faransa A Sansanin Sojan Ouallam A Nijar

A cikin wannan makon Faransa za ta fara janye sojojinta daga Jamhuriyar Nijar da sojoji suka yi wa juyin mulki, bayan da a watan da ya gabata Shugaban kasar Emmanuel Macron ya ce ya ki amincewa da "yin garkuwa da su" da masu Juyin mulkin suka yi.

WASHINGTON, D. C. - Hakan kuma ya kawo karshen hadin gwiwar soji da kasar ta yammacin Afirka.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron

Matakin janye dakaru 1,500 daga Nijar ya haifar da gibi a kokarin da kasashen yammacin duniya ke yi na dakile ayukan tada kayar baya na masu tsattsauran kishin Islama da aka kwashe shekaru goma ana yi. Har ila yau, hakan ya yi mummunar illa ga tasirin Faransa a yankin Sahel kuma zai iya bai wa Rasha damar fadada ikonta a kan manyan wuraren da ba su da tsaro a yankin.

Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar
Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar

A cikin wata sanarwa da ta aka fitar a ranar Alhamis, ma'aikatar tsaron Faransa ta ce sojojin za su koma kasar Faransa kuma za'a kammala kwashe sojojin a karshen wannan shekara.

Kin jinin juyin milki a Jamhuriyar Nijar
Kin jinin juyin milki a Jamhuriyar Nijar

Nijar dai ita ce babbar aminiyar kasashen yammacin duniya a yankin tsakiyar Sahel da ke kudu da hamadar Sahara har zuwa ranar 26 ga watan Yuli da aka yi juyin mulkin da ya kawo gwamnatin mulkin soja wadda ya bukaci Faransa ta fice daga kasar.

Macron ya kuma janye jakadan kasarsa daga Nijar.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG